11 Maris 2026 - 15:44
Source: ABNA24
Yadda Akai Jana’iza Da Bankwana Da Manyan Kwamandojin Shahidan Ramadan Iran + Bidiyo

A ranar tunawa da shahadar Imam Ali (AS) da yammacin yau tun daga Maidan Inqilab zuwa Maidan Mi’iraj ya cika da hawayen girmama ga rashin wadannan Shahidai; Inda mutanen Tehran suka dauki kwamandojinsu da suka yi shahada.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Dinbin Masu azumi ne a babban birnin kasar Tehran suka zo domin halartar jana'izar shahidan hare-haren jiragen sama na Amurka da gwamnatin sahayoniya na baya-bayan nan; MIliyoyin Mutane ne wanda daywa daga cikinsu har yanzu basu huta daga gaji raya daren Ghadr ba, amma sun halarci taron rakiyar shahidan; duk da yake an sanar da fara taron ne da karfe 13:30. A cikin wannan taron jana’iza akwai, gawarwakin shahidai da suka hada da Amir Janar Sayyid Abdul Rahim Mousavi, babban hafsan hafsoshin soji, Janar na Sojojin Juyin Juya Hali Muhammad Pakpour, babban kwamandan rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Amir Daryaban Ali. Shamkhani, Sakataren Majalisar Tsaro, Shahidi Amir Aziz Nasirzadeh, Ministan Tsaro da Tallafawa Sojoji, Sardar Shahid Muhammad Shirazi, Shugaban Ofishin Babban Rundunar Sojojin, Sardar Shahid Darehbaghi, Sardar Shahid Ali Tajik, Sardar Shahid Dawood Asgari, Sardar Shahid Husaini Mutlaq, Sardar Shahid Babaian, Sardar Shahid Helali da Sardar Shahid Rezaian ne aka jana’izarsu.

Baya ga wadannan kwamandoji, gawarwakin wasu gungun 'yan kasar na Tehran da suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai ta sama na baya-bayan nan suna cikin wadanda akai jana’izarsu cikin bakin ciki na jama'a; Daga cikinsu akwai iyalai da suka rasa mambobi da dama a lokaci guda. Masu Makoki sun ta rera taken kasa a gaban jami'ar Tehran tare da yin mubaya'a ga sabon jagoran juyin juya halin musulunci a dandalin Enghelab. Wani hoto na gagarumin kasancewar dinbin mutane a wurin jana'izar Shahidan yakin Ramadan yan biy anan kasa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha